1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Musulmi na bikin Sallar Layya

Yusuf Bala Nayaya
August 21, 2018

Mabiya addinin Islama a fadin duniya na bikin ranar Sallar Layya a wannan rana ta Talata yayin da sama da mahajjata miliyan biyu ke karkarewa da jifan shedan a can kasa mai tsarki ta Saudiyya.

https://p.dw.com/p/33S8z
Pakistan Eid al-Adha
Hoto: Reuters/F. Aziz

A wannan rana ce dai ta Talata mahajjatan ke tafiya zuwa Minna don jifan shedan abin da ke tuni da sa'ilin da Annabi Ibrahim A.S shedan ya so yi masa rada lokacin da Allah SWT ya nemi ya yanka dansa Annabi Isma'il kafin daga bisani Allah Ya fanshe shi da ragon layya.

A wannan rana ta karshe a aikin Hajjin dai har ila yau al'ummar Musulmi a fadin duniya na yin sallar idi ko Eid al-Adha inda Musulmai ke yanka abin da Allah Ya huwace masu na daga dabbobi kama daga raguna zuwa shanu ko rakuma kana naman a raba shi ga al'umma marasa karfi.