1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Al'ummar Najeriya za su fuskanci yunwa a shekarar 2025

Binta Aliyu Zurmi
November 9, 2024

Sama da al'ummar Najeriya miliyan 33 ne ke fuskantar barazanar yunwa a shekarar da ke tafe ta 2025.

https://p.dw.com/p/4mpWC
Nigerias Präsident Bola Ahmed Tinubu
Hoto: Greg Baker/AP Photo/picture alliance

A cewar wani rahoton gwamnatin kasar hadin gwiwa da na wasu hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin sa-kai, matsalar tsaro da ta sauyin yanayi gami da hauhawar farashin kayayyakin abinci na taka muhimmiyar rawa.

A cewar rahoton jihohi kasar 26 musamman wadanda ke arewaci da tsakiyar kasar ne ke a cikin wannan hadari.

Yanzu haka mutane sama da miliyan 25 ne ke fama da matsalar karancin abinci a kasar da ke da yawan al'umma sama da miliyan 200.

Karin BayaniTsadar rayuwa a arewacin Najeriya: