1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jaridun Jamus: Ambaliya da Sudan ta Kudu

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 20, 2024

Ambaliya a Afirka ta Yamma da zaben Sudan ta Kudu da sabuwar alakar Jamus da Kenya da kuma fargaba a yankin Kahon Afirka, sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/4ktqa
Najeriya | Maiduguri | Ambaliya
Mummunar ambaliya ta haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a Maidugurin NajeriyaHoto: Ahmed Kingimi/REUTERS

Jaridar Neue Zürcher Zeitung cikin sharhinta mai taken: Mummunar ambaliyar ruwa a yammacin Afirka, a Najeriya da Chadi da Nijar da kuma Mali miliyoyin al'umma sun fuskanci ibtila'in ambaliyar ruwa. A kwanakin da suka gabata, kallo ya koma yankin Arewa maso Gabashin Najeriya sakamakon mamakon ruwan sama da ya yi sanadiyyar mummunar ambaliyar ruwa. Tun da fari dai a makon da ya gabata wata madatsar ruwa ta balle a Maiduguri babban birnin jihar Borno bayan da ta cika ta tunbatsa, abin da yayi sanadiyyar ambaliyar da ta shafi sama da mutane dubu 200. Ba wai a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ne kawai aka fuskanci ibtila'in na ambaliya ba, su ma wasu kasashen Afirka sun fuskacin wannan balai'in a kwanakin baya-bayan. Ibtila'in ya shafi kasashen yankin Sahel na Mali da Nijar da Chadi, wadanda ke cikin bukatar agajin jin-kai. A cewar kungiyoyin bayar da agajin jin-kan, kimanin mutane miliyan guda ne ambaliyar ta tilasta barin gidajensu a Mali.

Sudan ta Kudu  | Shugaban Kasa | Salva Kiir | Zabe
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva KiirHoto: Brian Inganga/AP Photo/picture alliance

Sudan ta Kudu ta dage zabe: In ji jaridar die tageszeitung. Cikin sharhin da ta rubuta, ta bayyana cewa: Shugaba Salva Kiir ya sake bai wa kansa damar tsawaita lokacin shirya gudanar da zabe, wanda a abaya aka shirya gudanar da shi a watan Disambar wannan shekara. die tageszeitung ta ce: wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar, ta bayyana cewa ana bukatar karin lokaci domin shawo kan wasu al'amura kafin gudanar da zaben na Sudan ta Kudu. A yanzu zaben da aka shirya gudanar da shi a watan Disamban bana, an dage shi zuwa watan Disamba na 2026. Mahukuntan kasar sun bayyana cewa, tilas sai an samar da sabon kundin tsarin mulki da kuma kidayar jama'a. Wannan matakin dai inji jaridar bai zo da mamaki ba, domin kuwa sau biyu ke nan ana dage zaben na Sudan ta Kudu sakamakon jan kafa wajen shirya gudanar da shi da gwamnati ke yi.
Ita kuwa jaridar Welt online ta rubuta nata sharhin ne mai taken: "Riba ga kowanne bangare," Jamus ta cimma yarjejeniya kan batun 'yan ci-rani da Kenya. Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da shugaban kasar Kenya William Ruto sun amince da daukar ma'aikatan da ke da kwarewa a wasu fanononi da kuma mayar da 'yan Kenya da ba su da izinin zama a kasar zuwa gida. Jaridar ta ce: Yayin ziyarar Shugaba Ruto na Kenya a Jamus, Berlin da Nairobi na son su kara yawan 'yan ci-rani da suka fito daga kasar da ke yankin Gabashin Afirka, kuma a nan gaba za su yi aiki kafada da kafada. Tuni ministar harkokin cikin gida ta Jamus Nancy Faeser da na kasashen ketare na Kenya Musalia Mudavadi suka sanya hannu kan yarjejeniya, wadda za ta mayar da hankali wajen saukaka hanyoyin daukar ma'aikatan da suke da kwarewa a fannoni dabam-dabam daga Kenya. 

Jamus | Ziyara | Kenya | Shugaban Kasa | William Ruto | Ganawa | Olaf Scholz
Shugaban William Ruto na Kenya da shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: epd
Somaliya | al-Shabab
Mayakan al-Shabab na yin mummunan ta'adi a SomaliyaHoto: picture alliance / AP Photo

A sharhin jaridar Süddeutsche Zeitung ta mayar da hankali ne kan yankin kahon Afirka. Ta ce: Fargaba a yankin Kahon Afirka, Masar za ta tura kimanin sojoji dubu 10 zuwa Somaliya. Tana son ta taimaki gwamnatin Mogadishu, a yakin da take da masu tsattsauran ra'ayin kishin addini na al-Shabaab. Hakan, ka iya yin matukar tasiri a tashin hankalin da yankin ke ciki. Jaridar ta ce tuni wakilan gwamnatin Masar suka isa, a ranar 27 ga watan Agustan da ya gabata jiragen yaki sun sauka a babban filin jiragen sama na Mogadishu babban birnin Somaliya. Faya-fayen bidiyon da aka yada, sun nuna manyan jiragen dauke da inkiyar Masar da ma jami'an soja da kayan yakinta. Wannan dai ya kafa dambar sabuwar alaka tsakanin Mogadishu da Al Kahira. Tun bayan kifar da gwamnatin shugaban mulkin kama-karya Siad Barre a shekara ta 1991, Al Kahira ke da alakar tsaro da kasar da ke yankin Kahon Afirka. Sai dai tsarin ya gamu da tangarda, domin kuwa makwabciyar kasa Habasha da ke fada aji a yankin ta nuna adawarta da shi. A ganinta hakan na zaman barazana ga tasirin da take da shi da kuma kasancewar sojojinta a Mogadishu.