1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliya ta yi wa mutum 100,000 ta'adi a Kamaru da Chadi

October 25, 2022

Cutar amai da gudawa ko kuma Kwalara ta barke a tsakanin mutum sama da 100,000 da ambaliyar ruwa ta tilasta wa barin gidajensu a Kamaru da Chadi a cikin wannan wata na Oktoba.

https://p.dw.com/p/4Ienj
Hotan ambaliyar ruwa
Hotan ambaliyar ruwaHoto: Str/Xinhua/picture alliance

A yanzu haka dai wadanda abin ya shafa na cikin halin tasku, inda suke neman dauki a kan iyakokin kasashen biyu. Shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby ya sanya dokar ta baci, bayan bala'in na ambaliya a kan iyakar kasar da Kamaru da ya janyo asarar dukiya da gonaki masu tarin yawa. Shi ma shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya bayar da umurnin kai agajin gaggawa ga wadanda bala'in ya rutsa da su. Sai dai jama'an da abin ya shafa sun ce kayan agajin da aka kai musu ba su wadatar ba.

An dai kwashe tsawon mako guda ana sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya a garin Kousseri da ke kan iyakar arewacin Kamaru da Chadi. Mamakon ruwan saman dai, ya janyo tumbatsar Kogin Logone da shi ma ke kan iyakar kasashen biyu. Kimanin mutum 70,000 ne suka rasa gidajensu, ana kuma fama da matsalar karancin abinci sakamakon awon gaba da ambaliyar ta yi da dabbobi da gonaki.

Madou Simon Pierre, limamin Majami'ar Roman Katolika a birnin N'Djamena na kasar Chadi ya nunar da cewa dubban mutanen da ambaliyar ruwan ta tarwatsa mafi yawansu mata da kananan yara na neman mafaka a mujami'u.

Shugaban gwamnatin soji ta Chadi Mahamat Idriss Deby Itno
Shugaban gwamnatin soji ta Chadi Mahamat Idriss Deby ItnoHoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP

Daruruwan mutane ne dai ke karbar magani bayan barkewar cutar amai da gudawa a yankin na Chadi, kuma tuni cutar ta yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 22 yayin da kuma ake fargabar wasu da dama ma sun halaka bayan gaza kai wa ga kauyukansu saboda matsalar.

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana alhininta kan rasuwar 'yan gudun hijira uku cikin 81 da aka tabbar sun kamu da cutar ta amai da gudawa a sansanin 'yan gudun hijira na Minawao da aka ajiye 'yan Najeriya kimanin 76,000 da rikicin 'yan ta'addan Boko Haram ya tilasta wa barin gidajensu. Mai magana da yawun hukumar a Kamaru Helen Ngoh ta ce akwai bukatar taimakawa da kuma magance barkewar cutar a sansanin 'yan gudun hijirar a nan gaba.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul BiyaHoto: picture-alliance/AP Photo/Lintao Zhang

Majalisar Dinkin Duniyar dai ta ce ta samu rahoton bullar cutar amai da gudawa sama da 1,000, a makwabciyar kasa Najeriya da ke makwabtaka da kasashen na Kamaru da Chadi. Daraktan kula da cututtuka masu yaduwa a ma'aikatar kula da lafiyar al'umma  ta Kamaru Linda Esso ta bayyana cewa, asibitocin da ke yankunan kan iyakar kasar sun cika makil.

Gwamnatin Kamarun dai ta ce tana tattaunawa da mahukuntan Najeriya da Chadi domin su hada karfi waje guda a kokarin shawo kan annobar ta amai da gudawa.