SiyasaAfirka
Ambaliyar ruwa ta halaka kusan mutane 50 a Kenya
November 18, 2023Talla
Ambaliyar ruwan da zabtarewar kasa sun hala kusan mutane 50. Su dai Ambaliyar ruwa gami da zabtarewar kasa da aka samu sun kuma tilasta katsa tafiyar jirgin kasa zuwa garin Mombasa na Kenya mai tashar jiragen ruwa. A cikin wata sanarwar kamfanin kula da zirga-zirgar jiragen kasa na kasar ya ce haka ya faru sakamakon ruwan sama mai karfi na tsawon lokaci da aka tafka a kasar da ke yankin gabashin Afirka.
Sai dai kamfanin ya ce zai ci gaba da takaitaccen aikin sufurin fasinjoji, yayin da aka dakatar da daukacin dakon kaya gaba daya na wani lokaci. Jiragen kasan na dakon kaya daga tashar ruwan birnin na Mombasa da ke Kenya suke kai kayayyaki zuwa kasashen Ruwanda da Yuganda da kuma Sudan ta Kudu.