1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa ta yi ta'adi a Pakistan

Suleiman Babayo ZMA
August 5, 2022

Bayan sheka ruwan sama na tsaron kwanaki ambaliyar ruwa ta halaka kimanin mutane 450 a kasar Pakistan, yayin da hukumomi ke ci gaba da aikin ceto.

https://p.dw.com/p/4FC2y
Pakistan | Monsunregen in Karatschi
Hoto: Akhtar Soomro/REUTERS

Ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama da ake ci gaba da shekawa ta yi sanadiyar mutuwar kusan mutane 450 a kasar Pakistan cikin wata guda, inda galibi lamarin ya faru a yankin kusu maso yammacin kasar mai fama da talauci.

An tura hukumomin agajin gaggawa yankin gami da sojoji domin taimakon mutanen da ambaliyar ruwan ta ritsa da su.

Shi kansa Firaminista Shehbaz Sharif  na kasar ta Pakistan ya kai ziyarar gani da ido inda aka samu ambaliyar ruwa sannan ya ce gwamnati za ta yi duk abin da ya dace domin taimakon mutanen da lamarin ya shafa.