Ambaliyar ta kashe mutane sama da 100
September 4, 2022Talla
Kasar dai ta sha fama da ifta'i na ambaliyar daga watan Mayu zuwa watan Agusta kowace shekara wanda ke haifar mata da dimbin asara.
Alkalumman Majalisar dinkin Duniya sun yi nuni da cewa ambaliyar ruwan ta shafi fiye da mutane 2,200. Majalisar Dinkin Duniya ta kuma yi gargadin cewa ta yiwu alkalumma wandanda ambaliyar za ta shafa su nunku fiye da shekarar bara.
Ifta'in na bana dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin dambarwar siyasa da na tattalin arziki da ya ta'azzara sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a bara karkashin jagorancin Hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan.