1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amfani da Nijar don tafiya Turai

Mahaman Kanta
December 12, 2016

Bakin haure da ke kokarin shiga Turai ta teku kan yi amfani da hamadar sahara ta Jamhuriyar Nijar don kaiwa ga inda suka so a guda daga cikin kasashen da ke Turai.

https://p.dw.com/p/2UADM
Niger Agadez Sahara Flüchtlinge
Hoto: Reuters/Akintunde Akinleye

Jamhuriyar Nijar guda ce daga cikin hanyoyin da bakin haure daga nahiyar Afirka ke bi da nufin tsallaka wa zuwa nahiyar Turai domin samun ingantacciyar rayuwa. Mutanen da ke wannan tafiya wanda galibinsu matasa ne kan yi wannan tafiya mai hadari ce ta cikin hamadar sahara don isa Libiya daga nan kuma su yi kokarin ketara teku don shiga Turai.

Mafi yawan wadannan matasa kan rasa rayukansu a kan tekun wasu kuma da suka tsallake rijiya da baya kan kare ne a hannun jami'an tsaro na kan iyaka. Wakilinmu da ke Yamai Mahaman Kanta ya ziyarci wata tashar mota da ke birnin Yamai inda ya samu zantawa da wasu matasa da suka yada zango kafin cigaba da wannan tafia tasu. Guda daga cikin matasan dan kasar Senegal mai suna Sheriff da wakilin namu ya zanta da su ya shaida masa cewar ya sha matukar wahala kafin isa Nijar inda ya ce jami'a a kan haya kan karbi kudade a hannunsu. 

Shi kuwa Sulaiman Nadi dan kasar Gambiya ya shaidawa wakilinmu cewar dole ce ta sanya shi baro kasarsu don neman kudi ba wai don ya na so ba. Ga alama dai halin da ake ciki a Gambiya na musgunawa wanda ba sa tare da gwamnati ne ya sanya Sulaiman hijira don kuwa ya bayyana fatansa na ganin sabuwar gwamnatin kasar ta Adama Barrow ta yi aiki tukuru don inganta rayuwar talaka da nufin fidda su da kangin da suke ciki.

A daura da irin wadannan dalilai da matasan suka bayyana a matsayin dalilinsu na barin gida don zuwa Turai yin cirani da ma irin kalubalen da suke fuskanta a kan hanya, a hannu direbobin da ke jigilarsu sun bayyana irin kalubalen da su kan fuskanta. Sidi Sherrif da ke aiki da wani kamfanin sufuri a Yamai ya shaidawa DW cewar galibin matsalar da suka gamu da ita ba ta wuce ta rashin cikakkun takardu daga bangaren su bakin hauren da su kan dauka a motocinsu.