1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO ta yi gargadi kan Coronavirus

Zainab Mohammed Abubakar
March 24, 2020

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewar, akwai yiwuwar Amirka ta kasance wurin da cutar Corona za ta fi yin kamari, sanarwar da ke zuwa a daidai lokacin da aka kafa dokar hana zirga-zirga a Birtaniya.

https://p.dw.com/p/3Zxy9
USA New York Citiy | Coronavirus
Hoto: Reuters/A. Kelly

Sai dai a gunduwar Hubei da ke Chaina kuma tushen wannan annoba a watan Disambar shekarar data gabata, mahukunta sun sanar da sassauta dokar hana zirga-zirga, saboda raguwar yaduwar cutar. 

A bangaren tattali kuwa, harkokin kasuwanci sun rushe a kasashen Ostreliya da Japan da Yammacin Turai, inda a wani lokaci nan gaba a yau ne Amirka za ta gabatar da nata matsayin.

Mai magana da yawun Hukumar Lafiya ta Duniyar a birnin Geneva, Margaret Harris ta shaidar da cewa, yadda cutar ke ci gaba da yaduwa a Amirka abun ban tsoro ne.