1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Sasanta rikicin kasuwanci tsakanin Amirka da China

Suleiman Babayo MNA
May 20, 2018

Kasashen Amirka da China sun sasanta rikicin kasuwanci da ke tsakaninsu bayan ganawa ta manyan jami'an kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/2y1Tn
China Qingdao - Containerhafen
Hoto: picture-alliance/dpa/Imaginechina/Y. Fangping

Kasashen Amirka da China sun bayyana kawo karshen takaddama kan cinikayya tsakanin kasashen biyu da ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki a duniya. Bayan ganawa tsakanin manyan jami'an kasashen biyu a birnin Washington DC na Amirka kasashn sun amince da dakile shirin saka wa juna biyan kudaden shiga da kayayyaki, sannan China za ta kara yawan kayayyakin da take saya daga Amirka domin rage gibin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Mataimakin firaministan China Liu He wanda ya wakilci gwamnatin kasarsa a zauren tattaunawar ya ce matakin kasashen na zama nasara ga kowa.

Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta Amirka tana fata nan da shekara ta 2020 za a rage girman gibin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.