1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka da Koriya Ta Arewa sun fara tattaunawa a birnin Geneva

September 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuCa
Wakilan kasashen Amirka da KTA sun fara wani taro a birnin Geneva na kasar Switzerland inda suke tattaunawa a dangane da shirin nukiliyar KTA. Kamar yadda mai shiga tsakani na Amirka Christopher Hill ya nunar taron zai kuma tattauna kan yadda za´a sake fasalin tashoshin nukiliyar KTA ta yadda ba za´a iya amfani da su wajen kera makaman nukiliya ba. taron na yini biyu wani bangare ne na jerin taruka guda 6 da sassan biyu suka amince da shi. Manufa dai shi ne tsara wani shiri wanda dukkan bangarorin nan 6 dake shawartawa a dangane da kawo karshen shirin nukiliyar KTA zasu iya tattaunawa a kai.