1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Doha: Amirka ta cimma sulhu da Taliban

Zainab Mohammed Abubakar
February 29, 2020

Amirka da 'yan Taliban sun rattaba hannu kan yarjejeniya mai cikakken tarihi, wanda ka iya jagoranci Washinton janye dubban sojojinta daga Afghanistan.

https://p.dw.com/p/3YeiA
Katar Unterzeichnung Abkommen USA mit Taliban
Hoto: Reuters/I. al Omari

Tuni babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya isa Kabul, fadar gwamnatin Afghanistan, gabanin bukin rattaba hannu kan yarjejeniyar da ya gudana a Doha, babban birnin kasar Qatar.

A yayin ziyarar Stoltenberg, ya gana da shugaba Ashraf Ghani da sauran manyan jami'an gwamnatin Afghanistan, a cewar sanarwa data fito daga fadar shugaban kasar.

Bugu da kari, zai halarci taron manema labaru na hadin gwiwa da zai gudana, tsakanin shugaba Ghani da sakataren tsaron Amurka Mark Esper. Da isar sa Kabul din dai, sakataren na NATO ya gana da babban jami'in zartarwa Abdullah Abdullah.