1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na ci gaba da barin wuta a Iraki

Englisch-redAugust 18, 2014

'Yan kungiyar ta'addan IS da suka addabi kasashen Iraki da Siriya na fuskantar ruwan bama-bamai daga Amirka a yankunan da suka mamaye a Iraki.

https://p.dw.com/p/1CwED
Hoto: picture alliance/AP Photo

Kasar Amirka ta bayyana cewa ta fadada hare-haren da take kaiwa da jiragen yaki a yankin da 'yan ta'addan kungiyar IS suka mamaye a Iraki, a daidai lokacin da dakarun sojojin Kurdawa suka samu nasarar kwace wani babban Dam daga hannu 'yan ta'addan na IS. A makon da ya gabata ne dai 'yan kungiyar IS din suka samu nasarar kwace Dam din da ke garin Mosul daga hannun mayakan Kurdawan: Sai dai tun bayan da Amirka ta kaddamar da kai hari da jiragen yaki alkadarin kungiyar ta IS ya fara karyewa wanda kuma ya yi sanadin kwace Dam din daga hannunsu. Kwace Dam din na Mosul na zaman galaba mafi girma da aka yi a kan kungiyar IS din tun bayan da ta kaddamar da kai hare-hare a yankin arewacin Iraki cikin watan Yunin da ya gabata.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal