Amirka na rarrashin Saudiyya
November 4, 2013Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry yana birnin Riyadh, inda ya ke ganawa da Sarki Abdullah na Saudiyya. Ana dai ganin wannan ziyar ta Kerry a matsayin ƙoƙarin kwatar da hankalin mahukuntan Saudiyya, waɗanda a yanzu suka ruɗe, sakamokon jin cewa Amirka za ta maida hulɗar difalmasiya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A gefe guda Saudiyya na nuna fushi kan yadda gwamnatin Amirka ta kasa yin wani abu bisa yadda ta gyale Isra'ila ke ci-gaba da gina gidaje a yankunan Falashinawa. Abu na uku da Saudiyya ba ta ji daɗin Amirka ba shi ne, yadda Amirka taƙi ɗaukar matakan da za iya kawar da gwamnatin Bashar Alssad, wanda Saudiyya ke jagorantar ƙasashen Larabawa don mai da shi saniyar ware da kuma ganin bayansa.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mouhamad Awal Balarabe