Amirka ta daina bai wa Nijar tallafi
October 10, 2023Talla
Wani babban jami'n gwamnatinAmirka ya ce sun yanke shawara daina bai wa Nijar kudaden tallafi saboda a cikin watanni biyun da suka gabata sun bi duk hanyoyi da suka dace ba tare da cimma nasara ba, na ganin sojojin sun tabbatar da tsarin mulki na dimukaradiyya da suka hambarar, inda ya ce sakamakon haka Amirka ta kawar da ba da dala miliyan 442 na taimakon tattalin arziki ga Nijar. Babu dai wani karin bayyani da jami'in na Amirka ya yi bayan bayyana sanarwa dakatar da ba da tallafin kudin ga Nijar.