1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na daukar matakai kan Saudiyya

Yusuf Bala Nayaya
October 24, 2018

Donald Trump na Amirka ya bayyana abin da ke faruwa na kokarin gano wadanda suka kashe dan jaridar daga bangaren Saudiyya a matsayin rufa-rufa mafi muni da aka taba gani a tarihi.

https://p.dw.com/p/374ka
USA, Washington: Trump hält eine Kabinettssitzung im Weißen Haus
Hoto: Reuters/K. Lamarque

Kasar Amirka ta bayyana shiri na janye izinin zuwa kasar ta ga mutanen kasar Saudiyya da ake zargi na da hannu cikin badakalar kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi, abin da ke zuwa bayan da Shugaba Donald Trump na Amirka ya bayyana abin da ke faruwa na kokarin gano wadanda suka kashe dan jaridar daga bangaren Saudiyya a matsayin rufa-rufa mafi muni da aka taba gani a tarihi.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya dai yayin jawabinsa ga 'yan jam'iyyarsa a ranar Talata ya bayyana cewa dama kasar ta Saudiyya ta tsara ne a kashe dan jaridar sabanin cewa da ta yi fada ne ya jawo dalilin kisan nasa a ofishin jakadancinta da ke birnin Santanbul.