1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar tsaron Amirka ta gargadi mayakan Taliban

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
May 2, 2020

Rundunar tsaron Amirka ta gargadi mayakan kungiyar Taliban da ke ci gaba da kaddamar da hare-hare ba kakkautawa kan sojan kasar Afghanistan da su shiga taitayinsu inji wata wasikar bude

https://p.dw.com/p/3bhKx
Afghanistan Taliban-Kämpfer in Farah
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Wasikar mai shafi biyu da Kanal Leggett ya aikie wa Zabihullah Mujahid kakakain kungiyar Taliban, ya yi kira ga dukkan bangarorin biyu da su tsakaita wuta, yana mai cewa idan ba haka ba dakarun Amirka a shirye suke don fatattakarmayakan kungiyar na 'yan Taliban.

Sai dai ko a farkon wannan makon da ke shirin karewa babban kwamandan rundunar NATO da ke aikin tabbatar da tsaro a Afghanistan ya gargadi mayakan na Taliban da irin abin da ka iya faruwa daga baya, muddin suka ci gaba da kaddamar da hare-haren da suke aiwatarwa.

Kungiyar Taliban na matsa kaimi tare da kaddamar da hare-hare kan jami'an tsaron Afghanistan a baya bayan nan, makwanni bayan cimma wata yarjejeniyatr tsagaita wuta da Amirka a birnin Doka, wacce a cikinta 'ya 'yan kungiyar suka aminta da ci gaba da tattaunawa da hukumomin Kabul.