Amirka ta kakkabo makami mai linzami na mayakan Houthi
January 15, 2024Rundunar ta ce an harba makami mai linzamin ne zuwa wani jirgin ruwan sojin Amirka a ranar Lahadi. An dai kakkabo makamin ne a kusa da tashar ruwan Hudaida da ke Yemen.
Babu rahoton asarar rayuka ko barna. A baya-bayan nan Amirka da kuma kawayenta dai sun kaddamar da jerin hare-hare kan 'yan tawayen na Houthi da suke zafafa kai hare-hare kan jiragen ruwa na kasuwanci a Bahar Maliya. Sai dai mayakan sun sha alwashin daukar fansa.
Karin bayani: Bahar Maliya: Takaddamar Amurka da Houthi
Kungiyar Hezbollah ta ce farmakin da Amurka da mukarabbanta ke kai wa kan 'yan Houthi na Yemen ba komai zai janyo ba, face haddasa rincabewar rikicin yankin.
Karin bayani: Dalilan 'yan Houthi na barazana a Bahar Maliya
Tun bayan barkewar rikici a Zirin Gaza a watan Octobar bara, mayakan na Houthi da ke da iko da yawancin yankunan kasar Yemen ke kai hare-hare da jirage marasa matuka da kuma makamai masu Linzami mussaman kan Isra'ila.