Amirka ta tura da kayan yaki yankin Koriya
April 9, 2017Amirka ta tura da rundunar sojin ruwanta dauke da manyan makaman yaki a yammacin tekun Pacific a wani yunkuri na neman taka birki ga bazanara nukiliyar Koriya ta Arewa. Kakakin rundunar sojin ruwan Amirkar a yankin na Pacific Kwamanda Dave Benham ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa sun tura da ayarin jiragen ruwan yaki a karkashin jagorancin babban jirgin ruwan yaki na USS Carl Vinson da kuma rundunar sojin sama da wasu manyan jiragen yakin masu harba makamai masu linzami.
Sau biyar dai Koriya ta Arewa na yin gwajin makami mai lizzami a shekarun baya bayan nan a wani yunkuri na neman mallakar makamin nukiliya. Hukumomin leken asirin Amirka dai sun bayyana cewa Koriya ta Arewa na gab da mallakar makamin nukiliya mai cin dogon zango da ka iya ba ta damar harar Amirka kai tsaye cikin kasarta, nan kasa da shekaru biyu masu zuwa.
Sai dai a makon da ya gabata Shugaba Donald Trump na Amirka ya shaida wa takwaransa Xi-Jinping na Chaina cewa Amirka za ta yi gaban kanta wajen kalubalantar shirin nukiliyar Koriya ta Arewar ko da kuwa ba ta samu taimakon kasashen duniya ba.