Kwararru sun soki bukatar wani gwamna a Amirka
April 23, 2020Yayin wani taron tuntuba a fadar White House a wannan Alhamis din, shugaba Trump ya tsorata game da gaggawar bude wasu gurare da basa cikin muhimman cibiyoyin gudanar da rayuwar al'ummar kasar a yau da kullum. Shugaban na wannan jawabi ne bayan ya yi watsi da fargabar sake billar cutar a kasar nan gaba.
A nasu bangaren 'yan adawa da kwararru a harkokin lafiya sun yi Allah wadai da wannan kudiri na gwamna Kemp na jihar ta Georgia, bayan sun zarge shi da yin watsi da sharuddan da gwamnati ta gindaya wa kowacce jiha kafin bude harkokin kasuwanci.
Sakamakon gwaji da hukumar lafiya ta gudanar a ranar Larabar da ta gabata ya tabbatar da cewar akalla mutane 21,000 ne suka kamu da cutar ta Coronavirus a jihar ta Georgia yayin da mutane 840 suka rasa rayukansu.