Amirka za ta dauki mataki kan Koriya ta Arewa
August 29, 2017Talla
Amirka ta sanar da shirin daukar wani kwakkwaran mataki na musamman kan Koriya ta Arewa biyo bayan sabon gwajin makami mai lizzami da ta yi a wannan Talata da ya bi ta sarararin samaniyar kasar Japan. Jakadar Amirka a MDD Nikki Haley ce ta sanar da hakan a daidai lokacin da kwamitin sulhu na MDD ke shirin gudanar da wani taron gaggawa a wannan Talata domin nazarin barazanar nukiliyar Koriya ta Arewa.