1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta fara amfani da maganin Corona

November 23, 2020

Jamus ta nuna damuwarta kan samun maganin Corona a kasashe matalauta. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kiran hada karfi da karfe domin samar da maganin a koina a fadin duniya.

https://p.dw.com/p/3lhJ2
G20 Gipfel Saudi Arabien | Gruppenfoto digital
Hoto: Präsidentschaft G20 Saudi Arabien Pressestelle

Amirka za ta fara amfani da rigakafin COVID-19 a cikin watan Disemba mai kamawa. Hukumomin lafiyar kasar sun yanke wannan shawarar ce a daidai lokacin da annobar ke kara hallaka al'umma a kasar.

Kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya dai na da tabbacin samun allurar a kan kari, sai dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta bayyana damuwa kan samun maganin ga kasashe matalauta. Merkel ta yi kiran hada karfi wuri guda domin samar da maganin a ko'ina a duniya.

Shugabar gwamnatin ta Jamus ta ce duk da alkawarin shugabannin kungiyar kasashe masu arzikin masana'antu na duniya G20 kan wadatar da maganin na Corona har yanzu ba a cimma wata yarjejeniya ba a hukumance.

Taron na G20 da aka kammala a ranar lahadi ya tabo batutuwa da dama da suka hada da saukakawa kasashe masu tasowa bashin da ya yi musu katutu da kuma batun makomar kasashen Afirka.