NATO ta bukaci karin kudi
February 17, 2021Talla
Tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya sha alwashin janye dakarun sojojinsa daga kasar wanda ya lalata dangantaka tsakanin Amirkar da mambobin kungiyar, sai dai ana sa ran sabon shugaban kasar Joe Bide ka iya janye wannan kudurin, bayan sakataren harkokin tsaron kasar Lloyd Austin ya albarkaci taron.
Haka zalika daukacin kasashe mambobin kungiya na da ra'ayin cewa lokaci bai yi ba da zasu janye dakarunsu daga kasar ta Afghanistan.
Shi kuma a nasa bangaren babban sakataren kungiyar ta NATO Jens Stoltenberg ya ce dole ne kungiyar ta bukaci karin kudi domin cigaba da ayyukan tsaron da ta ke gudanarwa.