1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta sayarwa Saudiyya jiragen yaki 84

December 29, 2011

Gwamnatin kasar Amirka ta bayyana irin ribar da za ta ci bisa cikin jiragen yaki da za ta sarya wa kasar Saudiyya

https://p.dw.com/p/13bab
President Barack Obama shakes hands after receiving a gift from Saudi King Abdullah at the start of their bilateral meeting at the King's Farm in Riyadh, Saudi Arabia, Wednesday, June 3, 2009. (AP Photo/Gerald Herbert)
Shugaban kasar Amirka Obama da sarki Abdullah na kasar SaudiyyaHoto: AP

Fadar White House ta Amirka ta sanar da cewa cikin jiragen yaki da za ta sayarwa kasar Saudiyya zai samar wa Amirka kudi sama da dala biliyan 29. Hakan zai samar da guraben aiki dubu biyar ga Amirkawa, kana hakan zai zaburar da tattalin arzikin Amirka izuwa dala biliyan uku da rabi a ko wace shekara. Kakakin fadar White House Josh Earnest yace karkashin yarjejeniyar Amirka za ta sayarwa Saudiyya jiragen yaki 84, kana ta sabonta wasu jiragen 70 dake yanzu haka Saudiya. Kazalika za su sayarwa Saudiyya albarusai da horar da ma'aikatan jiragen. Kakakin na gwamnatin Amirka yace wannan cinikin ya kara bayyana kekkewar hulda da ke tsaknin Saudiyya da Amirka, a matsayin Saudiyya kawar ta Amirka a fannin tsaron yankin kasashen Larabawa baki daya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal