Amirka zata sayarwa Saudiyya da wasu kasashe 5 a Golf makamai masu yawa
July 28, 2007Talla
Jaridar Washington Post ta Amirka ta larbarto cewa Amirka zata karfafa kasar Saudiya da wasu kasashebiyar na yankin Golf a fannin aikin soji. Jaridar ta rawaito cewa a cikin shekaru 10 masu zuwa Amirka zata sayarwa kasashen bama-baman zamani da za´a iya sarrafa su da tauraron dan Adam da rokoki masu cin dogon zango da kuma jiragen ruwan yaki. Wannan cinikin makaman zai ci kudi dala miliyan dubu 20, kuma manufa a nan ita ce a karfafa kasashen na Larabawa kawanyen Amirka don su tinkari angizon da Iran ke kara samu a yankin na Golf. Jaridar ta ce da akwai kuma wani shiri na taimakawa Isra´ila da Masar da kudi dala miliyan dubu 43.