1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirkawa a gidan kason Koriya ta Arewa

Lateefa Mustapha Ja'afarSeptember 14, 2014

A wani mataki na sabon takun saka tsakanin kasashen Amirka da Koriya ta Arewa da basa ga maciji da juna, Koriyan ta yankewa wani dan Amirka daurin shekaru a gidan kaso.

https://p.dw.com/p/1DC4q
Hoto: Reuters/KCNA

Kotun koli a Koriya ta Arewa ta yankewa Matthew Miller dan asalin Amirka hukuncin daurin shekaru shida a gidan kaso tare da yin aiki mai tsanani, bisa abun da ta kira ayyukan tarzoma da ta sameshi da aikatawa a kasarta. Wannan dai na zuwa ne mako biyu bayan da Miller da wasu Amirkawa biyu suka nemi Washington ta kawo musu dauki. Miller na zaman dan Amirka na biyu da ke cikin hukuncin aiki mai tsanani a gidan kason kasar ta Koriya ta Arewa da basa ga maciji da juna da Amirkan. Mai shekaru 24 a duniya Miller ya shiga hannun mahukuntan Koriya ta Arewa ne a watan Afrilun da ya gabata bayan da mahukuntan kasar suka zargeshi da yaga takardar izinin shiga kasar wato Visa da kuma neman mafaka, abun da suka ce ya sabawa dokokin Koriya ta Arewan.