1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An take hakkokin dan Adam a 2021

March 29, 2022

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa Amnesty International, ta bayyana cewa an tauye hakkokin dan Adam a fannonin kiwon lafiya da 'yancin fadar albarkacin baki a shekara ta 2021.

https://p.dw.com/p/49Ba6
Rahoton shekara-shekara na Amnesty International
Amnesty International: An tauyewa mutane 'yancin kiwon lafiya da fadar albarkacin bakiHoto: Monika Skolimowska/dpa/picture alliance

A rahotonta na shekara-shekara da aka fitar, kungiyar ta Amnesty International ta yi nazarin halin da 'yancin dan Adam ke ciki a kasashe 154 na duniya. Kungiyar mai kare hakkin dan Adam ta ce kasashen duniya sun gaza yin katabus, a yayin da aka kyankyashi sababbin rigingimu da ke taba darajar mutane. Kazalika kungiyar a yayin taron manema labarai a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu ta ce rashin damuwa da jami'an gwamnatocin kasashe suka nuna, ya kara ta'azzara rigingimun da ake da su. Sai dai rikicin Rasha da Ukraine shi ne ya fi daukar hankalin rahoton na Amnesty International. Shugabar kungiyar Agnes Callamard ta zargi Rasha da aikata laifukan yaki a birnin Mariupol na Ukraine:"Kawanyar da aka yi wa birnin Mariupol da Amnesty ke kan bincike a kai, abin takaici ne. An hana mutane samun kayan agaji da kuma hana su kaurace wa rikicin da kiri-kiri ake taba fararen hula, wannan mu a wurinmu laifukan yaki ne.''Kungiyar ta Amnesty International dai ta ce wani abu da ke sosai mata rai shi ne yadda galibin laifukan take hakkin dan Adam din a shekarar da ta gabata zuwa yanzu, ba a hukunta masu aikata su ba. Rahoton kuma nunar da cewa kasashen Afirka na cikin wadanda fararen hula suka fi dandana kudarsu. Ta buga misali da kasashen Mali da Burkina Faso da Habasha da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Kamaru, inda Amnestyn ta ce ana fakewa da rikici ana wulakanta fararen hula. Kungiyar ta Amnesty International ta ce daga cikin tauye hakkin da dan Adam ya fuskanta a shekarar 2021, har da yadda kasashen duniya masu karfin tattalin arziki suka yi wa mutanensu riga-kafin corona yayin da suka mika wa kasashe matalauta ''sidin'' abin da ya rage na alluran da suka sarrafa domin mutanensu. Sai dai kuma duk da haka rahoton na shekara-shekara na kungiyar ta Amnesty International, ya siffanta zanga-zangar da mutane suka fito suka yi a kasashen Rasha da Indiya da Sudan da Lebanon a matsayin wani gagarumin ci-gaba da take fatan zai taimaka wurin tirsasa wa hukumomi mutunta dan Adam ba tare da la'akari da jinsi ko arzikinsa a cikin al'umma ba.

Ukraine I Yaki I Mariupol
Birnin Mariupol na kasar Ukraine da yaki ya daidaitaHoto: Mikhail Tereshchenko/TASS/dpa/picture alliance