1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta baiyana damuwa kan yawan kisan jama'a a Najeriya

August 11, 2021

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya, Amnesty international ta ce an hallaka sama da mutane 100 cikin wata guda a jihohin Kaduna da Plateau a tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/3yr51
Nigeria Viehdiebstähle in ländlichen Regionen
Hoto: DW/Katrin Gänsler

A gefe daya dai rundunar sojan Najeriyar ta ce akwai alamun haske, sakamakon gomman barayin shannu da ke ta hallaka a jihohin zamfara da kaduna da ma Jamhuriyar Niger. Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam na cewa lamarin na kara lalacewa sakamakon karuwar asarar rayuka a arewacin kasar a cewar kungiyar Amnesty International wadda cibiyarta ke a birnin Legas. 

Kungiyar ta ce daga 5 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Augusta, akalla mutane 112 ne aka hallaka a cikin rikicin 'yan bindiga da mazauna tuddai da kwari na jihohin kaduna da Plateau. Amnest tace rikicin dake kara fito da gazawar yan mulki na kasar fili ga gaza kare yan kasa a ko'ina, ya kai ga satar al'ummar yankin 116 bayan raba dubbai da muhallansu.

Rahoton kungiyar ya ce gwamnatin ta kyale kisan ramuwar gayya na cigaba da faruwa, bayan kisa da kwashe dukiyar jama'a da ke zama ruwan dare kama daga Zangon Kataf a Kaduna ya zuwa Bassa da Barikin ladi da Riyom a jihar Plateau.

Rashin da bashi iyaka a kokarin kare rayuwa da dukiyar al'umma, ko kuma ko in kula a cikin barazana mai girma dai, kama daga arewa maso gabashin tarrayar Najeriya ya zuwa arewa maso yamma dama tsakiyar cikin kasar, an kwashe sama da tsawon mako guda ana nuna hotunan mattatu da wadanda suka mika wuya ga jami'an tsaro a cikin wani sabon yanayin da ke nuna alamun nasara a bangaren jami'an tsraon kasar .

To sai dai daga dukkan alamu abun da ake gani a halin yanzu ya gaza burge masu kallon rikicin dake sauyin launi da salo a ko'ina a trrayar Najeriyar. Yahuza Getso na zaman wani masani kan harkar ta tsaro da kuma yace nasarar da jami'an tsaron ke ikirari na kama da wasan kwaikwayo.