Moroko ta gurfanar da 'yan ci-ranin da suka yi fada da Spain
June 29, 2022Masu fafutukar kare hakkin bil Adama sun nemi da a gaggauta gudanar da bincike mai zaman kansa kan mutuwar bakin haure 23 a yayin da suke kokarin tsallaka shingen wayar karfen da ya raba kasa Maroko da Spain a yankin Melilla. Kazalika 'yan fafutukar sun kara da nuna damuwa ga matakin da Maroko ta dauka na fara gurfanar da bakin haure 65 da ta tsare a matsayin masu laifi. Kakakin kungiyar Amnesty International mai kare hakkin dan Adam a Alberto De Fedro ya siffanta matakin da wani abin kunya da takaici a wannan lokaci da ake 'ikirarin mutunta hakkin bil Adama.'
"Abin takaici ne a siffanta bakin haure da masu laifin da za a dinga kashewa; ana daurewa, tamkar wasu 'yan ta'adda'' in ji De Fedro. Ya ce matakin hana 'yan ci-rani cimma burinsu babu abin da zai haifar in ba karin tashin hankali ba a nahiyar Afirka.
Sai dai ministan kula da harkokin cikin gida na kasar Maroko, Abdulwafi Latfeef, ya kare matakin gwamnatin kasar inda ya ce ''an gurfanar da yan ci-ranin ne kan laifukan da suka danganci tayar da tarzoma.'' Ya ce ''Idan za mu bar su su yi abun da suke so, to za su jefa kasarmu cikin tarzoma da tashin hankali."
Mahukuntan Moroko sun ce mutuwar bakin-hauren da dama ta biyo bayan tirmitsitsin da aka yi a lokacin arangamarsu da jami'an tsaron kasar. Lamarin da ya faru a ranar Jumma'a ya yi sanadin jikkatar jami'an kwantar da tarzoma 77. To amma rahotanni sun ce 'yan ci-rani kusan 130 sun yi nasarar tsallakawa Spain.
Kasar Spain, wacce tun da farko ta yi amfani da karfi wurin tarwatsa 'yan ci-ranin bayan umurnin da firaministan kasar ya bayar, tuni ta bayar da hakuri, har ma ta nemi afuwar abin da ya faru. Duk da haka, Kungiyar Tarayyar Afirka, AU, ta bayyana kaduwarta kan abin da ta kira musguna wa bakin-haure ta kuma bukaci da gudanar da bincike kan lamarin.