Amnesty ta zargi Shell da gurɓata muhalli a Najeriya
August 3, 2012Ƙungiyar kare hakin bil adama Amnesty International ta ce babbar kasawa ce kamfanin mai na shell ya yi, akan rashin bayar da sahihan baiyanai akan binciken da ya gudanar dangane da aikin hakar man da ya ke yi a yankin Naija Delta na Tarrayar Najeriya wanda ya janyo mumunar gurɓata muhali a wani ɓangaran na man fetir da ke tarara a cikin gonaki.
A cikin wata sanarwar da ta baiyana daraktar ƙungiyar Audrey Gauhran, ta ce abin takaici ne dangane da yadda kamfanin ya musunta cewar ba shi ne ke da alhakin malalar man ba a ƙauyen Bodo Greek a cikin watan Yuni da ya gabata.wanda ya lalata gonaki manoma kamar dubu 11 dake zaune a yankin wanda kuma daga bisani binciken kungiyar ya gano cewar bututun man, na shel sun yi tsatsa ne abinda ya hadasa tarrara man. Kamfanin dai na shell na zargin barayi masu fashin bututu domin satar man, da laifin hadasa lamarin.
Mawallafi : Abdourahaman Hassane
Edita Abullahi Tanko Bala