Najeriya Amnesty ta zargi sojojin kasar
November 1, 2018Kungiyar kare hakin jama'a ta Amnesty International da ta bayyana bacin ranta a kan abin da ta kira kisan da ya sabawa doka da aka yi wa ‘yan Shi'a a Najeriyar, ta ce tana da shaidu da suka nuna sojojin sun yi amfani da manyan bindigogi wanda jami'anta sun gani da ido a wurare biyar da suka ziyarta a Abuja. Kiraye-kiraye na lallai sai gwamnati ta hukunta sojojin da suka aikata laifin ya sanya tunkarar rundunar sojan don jin ta bakinsu a kan lamarin, inda mukadashin kakakin rundunar tsaron Najeriyar Brigadier Janar John Agim ya bayyana cewar.
Ya ce: ''sojojin nan fa an samesu ne a bakin aikinsu mu ba za mu yi wani abu da zai cuci kungiyar ‘yan Shia ba, ai suna da mambobi har a soja, amma idan suka zo za su hargitsa zaman lafiya ba za mu sa ido ba. ''
Kafin wannan dai ‘yayan kungiyar sun bizne wasu daga cikin mutanen da aka kashe a yanayi na nuna alhini musamman ga ‘yan uwan mutanen da aka kashen. Tun daga shekara ta 2015 dai lamura na ci gaba da muni a duk lokacin da aka yi arangama tsakanin sojojin da ‘yan Shi'a a Najeriya. Inda suka ce za su ci gaba da tatakin ne saboda har yanzu gwamnatin Najeriya na tsare da shugabansu Sheikh Ibrahim Zakzaky.