Amnesty ta zargin Gambiya da take haƙƙin ɗan Adam
July 21, 2011Bisa alada dai shugaba Jammeh na ƙasar ta Gambia ya kan keɓe ranar 22 ga kowanne watan yuli amatsayin ranar da ya kira wai ta yanci, sai dai kuma ta la akari da yadda haƙƙin bil adama ke fuskantar barazana daga mahunkuntan ƙasar, ware wannan rana ya zama tamkar wani nutso da malafa. Shugaban dai ya kan yi amfani da tsauri wajen murƙushe dukkan masu adawa da shi ƙasar, kamar dai yadda Tawanda Hondora, mataimakin darektan ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Amnesty international,mai lura da nahiyar Afrika ya bayyana:
"Haƙƙin bil adama a Gambia yana cikin wani mummunan yanayi, 'yan jarida da 'yan siyasa dake hamayya sune suka fi gamuwa da garari, kuma da dama daga cikinsu ana zargin su ne da laifin cin amanar ƙasa. Ana yawan kai wa 'yan jarida hari tare da kama su a jefa su a kurkuku, inda ake gana musu azaba."
Har ila yau rahotan na Amnesty ya nunar da cewar mutane da dama ne ke rasa rayukansu a sakamaon amfani da ƙarfi da jama'in tsaron ƙasar ke yi, harma ƙungiyar ta ce tana da cikakken rahotan yadda aka hallaka wasu ɗalibai da 'yan jarida da kuma wasu 'yan ƙasashen waje.
Haka ne ma ya sa ƙungiyar tayi kira ga babbar murya ga ƙasasshen duniya dake da tasiri ga mahukuntan ƙasar da su ringa sanya batutuwan kare haƙƙin biladama a gaba. Tawanda Hondora yace yana da matuƙar muhimmanci ƙasashen dake cikin gamayyar tarayar Turai kamar Jamus da Faransa dama waɗanda ba sa ciki kamar Amurka da su yi amfani da tasirinsu ga mahukuntan ƙasar wajen nunar dasu akan halin ha ulai da haƙƙin bani adama ke ciki.
Bincike ya nunar da cewa mahukuntan ƙasar na yin amfani da gana wa mutane azaba wajen tilasta musu amsa wani laifi. Ƙungiyar Amnesty International ta bayyana cewa maimakon ƙasar ta Gambia ta ringa yin bikin ranar 'yanci wanda babu shi a Kasar gara ta ringa yin amfani da wannan rana ta 22 ga watan yulin ko wacce shekara wajen kiyayewa da haƙƙin bil adama. Aranar Talatar da tagabata ma dai wasu 'yan jarida su 3 tare da wasu 'yan adawan ƙasar dake gudun hijira a ƙasashen waje,an zartas musu da hukunci bisa tuhumar su da aka yi da cin amanar ƙasa, ciki kuwa har da tsohon shugaban ƙungiyar 'yan jaridun ƙasar, bisa laifin rarraba wasu riguna da a jikinsu aka rubuta kalaman neman sauyin mulkin kama karya a ƙasar Gambia.
Mawallafi: Nasiru Zango
Edita: Ahmad Tijani Lawal