1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta samu Trump da laifukan tuhume-tuhumen da ake masa

May 31, 2024

Wata Kotu a birnin New York na Amirka ta samu tsohon shugaban kasar, Donald Trump da laifukan tuhume-tuhume 34 da ake masa.

https://p.dw.com/p/4gToz
Tsohon Shugaban Kasar Amirka, Donald Trump
Tsohon Shugaban Kasar Amirka, Donald TrumpHoto: Steven Hirsch/New York Post/AP/pool/picture alliance

Daga cikin tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon shugaban kasar, har da karya da yayi a kan harkokin kasuwancinsa da kuma kudin toshiyar baki da ya bayar kan alakarsa da wata mai fina-finan batsa, Stormy Daniels.

Karin bayani: An fara shari'ar Donald Trump kan zargin bada toshiyar baki

A lokacin da yake magana a zauren kotun bayan kamalla zaman shari'ar, Shugaba Trump yi ikrarin cewa an tafka magudi kana sakamakon shari'ar babban abun kunya ne. Shugaba Trump ya kara da cewa babban hukunci shi ne wanda Amirkawa za su yanke, a lokacin da za su zabi sabon shugaban kasa, a ranar biyar ga watan Nuwambar 2024.

Har wayau, kwamittin yakin neman zabe na Shugaba Joe Biden ya yi maraba da sakamakon shari'ar, inda kwamittin ya ce hakan ya nuna karara babu wanda ya fi karfin doka. Ana sa ran jam'iyyar Republican ta sanar da sunan Shugaban Trump a matsayin wanda zai mata takarar shugaban kasa a yayin babban taronta.