Amurka ta gargadi Koriya ta arewa game da sake yin wani gwajin na nukiliya
October 17, 2006Talla
Kasar Amurka ta yi gargadi ga Koriya ta arewa a game da barazanar sake yin wani gwajin na makaman nukiliya,ta kuma yi watsi da ikrarin da Koriyan tayi na cewa takunkumin yana matsayin yaki ne aka kaddamar akanta.
Yayinda sakatariyar harkokin wajen Amurkan, Condoleeza Rice ke ziyara a yankin,babban wakilinta akan batutuwan Koriya Christopher Hill yayi gargadin cewa gwamnatin Amurka zata dauki duk wani gwaji da Koriya ta arewa zata sake yi a matsayin amsarta ga kasasahen duniya wanda yace ba zaiyi mata dadi ba.