An alƙawarta wa Siriya dala miliyan dubu 2.4
January 15, 2014Ƙasashen yamma da na Larabawan yankin Gulf sun yi alƙawarin ba da sama da dalar Amirka miliyan dubu 2.4 a matsayin agaji ga ƙasar Siriya. Ƙasashen sun ɗauki wannan alkawari ne a taron ƙasa da ƙasa da aka gudanar a Kuwaiti a wannan Laraba da nufin tara kuɗin taimaka wa Siryia wadda yaƙin basasa ya ɗaiɗaita. Majalisar Ɗinkin Duniya wadda ta shiyar taron ta yi fatan samun dalar Amirka miliyan dubu 6.5 a shekarar 2014, wanda aka ƙaddamar a watan da ya gabata, wanda kuma shi ne wani tallafi mafi girma a tarihin Majalisar ta Ɗinkin Duniya. Irin wannan taro da aka gudanar a bara kashi 70 cikin 100 na kuɗaɗen da aka alƙawarta ya shiga batul-malin Majalisar Ɗinkin Duniya. Gamaiyar ta ƙasa da ƙasa ta yi kiyasin cewar rikicin ya mayar da aikin raya ƙasa a Siriya baya da kimanin shekaru 35, inda yanzu haka rabin al'ummar ƙasar ke rayuwa cikin matsanancin talauci.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane