An amince da sanarwar bayan taro kan muhalli a Kanada
December 10, 2005Jim kadan gabanin kawo karshen babban taron duniya akan yanayi a Kanada, kusan dukkan kasashe dake halartar taron sun amince akan cimma wani burin kare muhalli kafin shekara ta 2008. Kasashen sun ce ya kamata a gabatar da wata sabuwar yarjejeniya wadda zata maye gurbin yarjejeniyar birnin Kyoto. A shekara ta 2012 yarjejenyiar ta Kyoto zata kare aiki. A cikin daftarin sanarwar bayan taro a birnin Montreal, an bayyana sauyin yanayi a matsayin wani babban kalubale da ya kamata a mayar da hankali akai. To sai dai har yanzu Amirka ta ki amincewa da wata yarjejeniya dangane da kare muhalli. Tsohon shugaban Amirka Bill Clinton ya soki lamirin gwamnatin Washington da cewa Amirka wadda ke da kashi 4 cikin 100 na al´umar duniya baki daya, ita ce kuma ke fid da kashi daya cikin hudu na iskar dake dumama doron kasa.