An ayyana dokar ta baci kan cutar Corona
January 31, 2020Talla
Yayin ayyana dokar ta bacin, shugaban Hukumar Lafiyar ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya nunar da yadda wannan annoba ta haifar ta fargaba tsakanin al'ummar sauran kasashe. Daga nan sai ya jaddada aniyar hukumar lafiyar ta ci gaba da yaki da cutar ta corona domin gudun billar ta a kasashen da suke da rauni a bangaren kula da lafiya.
Kasar Chaina ta tabbatar da kamuwar mutanen da yawansu ya kai 9,692 bayan mutuwar wasu 213 yayinda akalla 43 ke cikin mawuyacin hali, mafiya yawan wadanda cutar ta kama na zaune ne a birnin Wuhan da ke yankin Hubei na kasar.
Yanzu haka dai masana lafiya sun bayyana samun billar cutar a kasashen Faransa da Japan da Jamus da Kanada da Koriya ta Kudu da kuma Vietnam.