1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta ba da izinin bude masallatai a Jamus

Gazali Abdou Tasawa
April 30, 2020

Kotun kolin kasar Jamus ta ba da umurnin sake bude masallatai da sauran guraren ibada wadanda gwamnatin kasar ta rufe a baya a wani mataki na yaki da yaduwar annobar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3baYJ
Deutschland Hamburg | Freitagsgebet in der Al-Nour Moschee
Hoto: Zentralrat der Muslime in Deutschland

Wata kungiyar addinnin Islama ce ta arewacin kasar ta kalubalanci matakin gwamnatin kasar ta Jamus na hana gudanar da sallar Juma'a a wannan lokaci na azumin Ramadana a wani masallaci na Jihar Lower Saxony.

 A wani zama da ta gudanar a jiya Laraba, kotun kolin kasar ta Jamus ta dauki matakin soke hukuncin da wata kotun da'a a jihar ta yanke a baya na hana gudanar da taruka har a wuraren ibada na Musulmi da Kiristoci da na Yahudawa da nufin hana yaduwar annobar Coronavirus.

A lokacin gabatar da hukuncin dai kotun kolin ta ce matakin da aka dauka a baya ya keta haddin 'yancin gudanar da ayyukan ibada wanda kundin tsarin mulkin kasar ta Jamus ya tanada. A kan haka ne kotun ta ba da izinin ci gaba da taruwa a wuraren ibada duk da cewa cutar na ci gaba da yaduwa a kasar. Sai dai kotun ta gitta sharadin daukar matakan kariya a wuraren ibadar.