1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Belin: Bude filin jirgi na kasa da kasa

Abdullahi Tanko Bala
October 31, 2020

A jamus an bude sabon filin jirgin sama na kasa da kasa a birnin  Berlin shekaru tara bayan wa'adin da aka shirya bude filin jirgin saman tun da farko.

https://p.dw.com/p/3khT4
Deutschland Kunst am Bau - Flughafen Berlin Brandenburg | «The Magic Carpet» von der US-Künstlerin Pae White
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture-alliance

Filin jirgin saman wanda aka bude a wannan Asabar a wani kwarya kwaryar biki ya sami halartar jama'a 'yan kalilan da fasinjoji saboda annobar Corona.

Shekaru 30 da suka gabata aka kaddamar da filin jirgin saman wanda aka yi ta dage bude shi har sau bakwai a baya wanda kuma ya kasance mafi daukar hankali da tabargaza ta cin hanci da rashawa.

An kashe tsabar kudi euro biliyan shida wajen gina shi. An kuma sanya wa filin jirgin suna filin jirgi na Berlin-Brandenburg, Willy Brandt tsohon shugaban gwamnatin Jamus ta yamma wanda aka fi sani da BER a takaice.