An fara zabe a kasar Zimbabuwe
July 30, 2018Yayin da 'yan takara 23 ke neman shugabancin kasar a Zimbabuwe 'yan takara biyu su ake tsammanin daya ya kai labari, Nelson Chamisa dan shekaru 40 matashi daga jam'iyyar MDC mai adawa da Shugaba Emmerson Mnangagwa dan shekaru 75 da ya gaji Mugabe a karagar mulki.
Wannan zabe dai ana ganin za a fafata sosai tsakanin wadannan 'yan takara ganin yadda kuri'ar jin ra'ayin jama'a a makon da ya gabata ta nunar da cewa Mnangagwa da aka fi sani da "Kada" ko "The Crocodile" a Turance ya bai wa Chamisa rata ta kashi uku ne cikin dari kacal.
Tun da misalin karfe bakwai, biyar ke nan agogon GMT aka bude tashoshin kada kuri'ar yayin da ake sa rai mutane milyan biyar za su yi zabe don neman shugabanci da zai iya fitar da kasar daga yanayi na tabarbarewar tattalin arziki.