An bude tashoshin zaben Kenya
March 4, 2013Tun da sanyin safiyar wannan Litinin aka bude tashoshin zaben kasar Kenya, tare da samun dogayen layuka na masu kada kuri'a, domin zaben wanda zai jagoranci kasar na gaba.
Ana gudanar da zaben da na 'yan majalisu tare da kuma na yankuna. Akwai 'yan takara takwas da ke zawarcin kujerar shugaban kasar, amma za ayi fafatawa mai zafi tsakanin manyan 'yan takara biyu ne, Firaminista Raila Odinga da mataimakin Firaminsitan Uhuru Kenyatta.
An samu rahoton tashin hankali a garin Mambassa mai tashin jiragen ruwa, yayin da wasu tsageru su ka hallaka kimanin 'yan sanda hudu da sanyin safiya. 'Yan sandan sun mayar da martani kan hari.
Wannan shi ne karon farko da 'yan kasar ta Kenya ke gudanar da zaben bayan shekaru biyar da samun tashin hankali da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da ya gudana. A yanzu haka Uhuru Kenyatta da mai masa takaran mataimaki William Ruto na cikin wadanda ke fuskatan tuhuma akan duniya kan wannan tashin hankali da ya janyo mutuwan fiye da mutane 1,100, sannan wasu dubban su ka rasa matsugunai.