Amirka ta tsoratar game da illolin wasu kasuwannin Chaina
April 23, 2020Talla
Sabuwar cutar ta COVID-19 dai, ta samo asali ne daga wata kasuwar namun daji dake birnin Wuhan na kasar ta Chaina a shekarar bara. Annobar Corona Virus ta karade duniya cikin kankanin lokaci tare kashe mutanen da yawansu ya kai 180,000 bayan jikkata sama da mutane miliyan biyu a kasashe daban-daban, mumunan ibtila'in da ya haifar da tsaiko a kowanne bangare.