An bukaci da´a dauki matakan kare muhalli a Jamus
December 28, 2006Talla
Babban jami´i a a ofishin kula da muhalli na Jamus, Mr Andreas Troge ya bukaci da´a kayyade yawan gudun da abubuwan hawa zasu yi, a manyan titunan kasar na bai daya.
Kirkiro wannan doka a cewar babban jami´in ka iya rage yawan gurbatacciyar Iska da abubuwan hawan ke fitarwa.
Mr Andreas Troge ya kara da cewa kayyade gudun kilomita 120 a awa daya ga abubuwan hawa, hanya ce da zata rage gurbatacciyar Iskar da kashi 10 zuwa 30 cikin dari.
Ya zuwa yanzu dai tuni, Jam´iyyar The Greens tayi maraba da wannan shawara.
Idan dai an iya tunawa wannan jam´iyya ta The Greeens, Jam´iyya ce data shahara a manufofinta wajen kare muhalli.