An bukaci rundunar sojin Najeriya ta biya diyya
November 11, 2024Fiye da shekara guda kwamitin ya kwashe yana gudanar da bincike a kan zargin da ya tada hankali sosai a Najeriya cewa sojoji sun rika tilasta wa mata fararen hula da suka kama a Maiduguri zubar da ciki
Zargin da binciken kamfanin dillancin labaru na Reuters ya gudanar, ya bankado cewa sojojin Najeriya sun tilasta wa mata 10,000 zubar da ciki da ‘yan Boko Haram suka yi masu a lokacin da suke hannunsu, sannan sojojin sun kashe wasu yaran da aka haifa ba bisa doka ba da ma wasu zarge-zarge na kisa da take hakokin jama'a. Kwamitin mai wakilai goma ya gudanar da bincike mai zurfi a kan wannan zargi. Mai shari'a Abdu Aboki shine shugaban kwamitin.
Karin BayanI:Amnesty ta bayyana damuwa da kisan fararen hula a Najeriya
‘'Yace abinda muka gano shine kazafin da aka yiwa sojojijn Najeriya yawancinsu karya ne domin masu kazafin yawancinsu basu zo sun bada shaida ba kaman su Reuters din da suka yi zargin".
Kan batun zargin kisan jama'a kuwa shugaban kwamittin ya ce
‘'Eh akwai an samu a wani gari da ake kira gasarwa inda aka ce sojojin Najeriya sun kashe wasu yara shaida, bincike ya nuna gaskiya ne hakan ya afku don haka mun ce a biya diyya ga mutanen da abin ya faru akan su''.
Karin Bayani:Za'a binciki sojojin Najeriya
Kwamitin ya shafe watani 18 yana gudanar da wannan aiki inda ya ziyarci sassa hudu na jihar Borno da aka yi wannan zargi. Mutane 199 suka bayar da shaida a gaban kwamitin 154 maza sai mata 45 shaidar da suka dauki saoi'i 109 ana gabatarwa. An dai mika rahoton ga hukumar kare hakin jama'a ta Najeriya wacce aka dora wa nauyin kafa kwamitin binciken.Mr Tony Ujukwu shine shugaban hukumar kare hakin jama'a ta Najeriyar.
‘'Aikin kwamitin binciuke a kan zarge-zage na take hakokin jama'a a yankin arewa maso gabashin Najeriya ya nuna aikin da hukumar kare hakin jama'a ta Najeriya ke yi na tabbatar da an kare hakokin jama'a domin wannan kwamiti an dora masa nauyin duba take hakkokin jama'a a kan mata da yara kanana. Hukuma ta gamsu da irin sadaukar da kai da kwamitin ya yi inda ya mika rahonsa, wannan zai taimaka wa aiki a tsakanin hukumomi wajen aiyyukan jin kai a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Hukumar kare hakin jama'a za ta tabbatar da aiwatar da wannan rahoto''.
Karin Bayani: An zargi Sojojin Najeriya da cin zarafin jama'a
Kungiyoyin kare hakkin jama'a na Amnesty International da na Human Rights Watch sun sha gudanar da irin wannan bincike tare da zargin take hakkokin jama'a da jami'an sojojin kasar ke yi. Sun bukaci a kafa kwamiti mai zaman kansa ba wanda ke da alaka da gwamnati irin wannan ba. Comrade Shehu Sani da ke fafutukar kare hakkin jama'a yace akwai sauran aiki ga jami'an tsaro ma da ma alummar Najeriya.
Kodayake jami'an soja da suka hallarci kaddammar da rahoton sun ki cewa uffan, amma tun kafin kai wa wannan mataki rundunar sojan Najeriyar ta musanta wannan zargi da aka yi mata. A yanzu suna murna da sakamkon rahoton.