1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jamhuriyar Nijar ta buka ficewar wasu dakaru

Gazali Abdou Tasawa SB/LMJ
January 30, 2024

Hukumomin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar sun kori wasu sojojin rundunar zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Turai a Sahel wato EUCAP-Sahel da ma shugabar kungiyar daga kasar.

https://p.dw.com/p/4bqCV
Sojojim kasashen ketere da ke Jamhuriyar Nijar
Sojojim kasashen ketere da ke Jamhuriyar NijarHoto: ALAIN JOCARD/AFP/Getty Images

Wannan na zuwa ne lokacin da ya rage sama da watanni hudu , wa'adin da hukumomin suka bai wa rundunar na ficewa daga cikin kasar ya cika. Kazalika gwamnatin kasar ta Nijar ta kori babban wakilin hukumar kula da samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya wato PAM a kasar.

A cikin wata wasika ce da ministan cikin gida na kasar Nijar Janar Mohamed Toumba ya rubuta kana ya aika wa shugabar rundunar da EUCAP-Sahel  reshen Nijar ya sanar da bai wa sojojin 15 umurnin ficewa daga kasar a cikin sa'oi 72. Yana mai zargin sojojin da shigowa cikin kasar ta Nijar ba tare da sanar da mahukunta ba, alhali tun a ranar hudu ga watan Disamban da ya gabata, suka soke yarjejeniyar da ta hada Nijar din da kungiyar ta Tarayyar Turai kan zaman wannan runduna ta Tarayyar Turai tare ma da ba ta wa'adin watanni shida domin ficewa daga kasar baki daya kamar yadda yarjejeniyar girke rundunar ta tanada.

Sojojim kasashen ketere da ke Jamhuriyar Nijar
Sojojim kasashen ketere da ke Jamhuriyar NijarHoto: Sam Mednick/AP Photo/picture alliance

Ko a karshen makon da ya gabata mahukuntan kasar ta Jamhuriyar Nijar sun kori shugaban rundunar baki daya Katja Dominik 'yar kasar Jamus, inda suka tare ta tun a filin jirgin saman Yamai dawowar ta daga balaguro suka tilasta mata komawa kai tsaye daga inda ta fito. Kuma Malam Ismaeila Mahamadou shugaban kungiyar Debout niger da ke goyon bayan gwamnati, ya yaba da matakin mahukuntan yana mai cewa. Sai dai kuma ba duka ‘yan nijar suka yaba da wannan mataki na hukumomin mulkin sojan kasar ba na korar sojojin wannan runduna ba.

A share daya kuma hukumomin mulkin sojan kasar ta nijar sun kori babban wakilin hukumar samar da abinci ta MDD a Nijar wanda shi ma suka tare shi a filin jirgin sama na birnin Yamai lokacin dawowarsa daga balaguro inda suka umurci nan take ya fice daga kasar. Sai dai Malam Isma'ilou Aboubacar wani matashin dan fafutika a nijar ya ce akwai bukatar mahukuntan si yi wa ‚yan kasa bayani kan wannan mataki.

Kawo yanzu dai hukumar ta PAM ba ta kai ga cewa uffan ba a game da matakin korar babban wakilin nata a nijar a yayin da daga nata bangare kungiyar EU ta nuna rashin jin dadinta a game da matakin mahukuntan kasar ta nijar na korar shugabar rundunar ta Sahel duk da cewa wa'adin kammala ficewar rundunar da doka ta tsaida bai cika ba.