An cafke matar al-Baghdadi a Lebanon
December 2, 2014Talla
Majiyar ta ce ana tsare da matar da kuma ɗanta a wata cibiyar hukumar leƙen asiri ta soja da ke a garin Yarze kusa da Beyrouth tun kwanaki goman da suka wuce.
Matar wacce 'yar asilin ƙasar Siriya ce an kamata da ɗanta mai kimanin shekaru takwas zuwa tara a kusan daga garin Arsal tare da fasfo na jabu. A cikin wata Yunin da ya gabata ne al Baghdadin Ƙungiyarsa ta IS ta yi iƙirarin kafa daula a cikin ɗaukacin ƙasashe musulmi.Yanzu haka dai ƙungiyar na kai mummunar hare-hare a Iraƙi da Siriya.