An ceto daliban sakandaren Kankara
December 18, 2020Kimanin yara sama da dari uku ne gwamnatin jihar Katsina da ke Arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta ceto su daga hannun masu garkuwa da mutane. Gwamnan jihar Alhaji Aminu Bello Masari ya ce illahirin yaran na karkashin kulawar jami'an tsaro yayin da kuma ake duba lafiyarsu gabanin hannanta su ga iyayensu. Sai dai abin da ba a tabbatar da shi ba shi ne gaba daya yaran ne aka ceto ko akwai saura tare da sanin an biya kudin fansa ko ko a'a ba.
Shugaba Muhammadu Buhari a na sa bangaren ya yaba da wannan ci gaba da aka samu, wanda ya bayyana da wani abin sanyaya zuciya ga iyayen yaran da ma kasa baki daya. Yankin na Arewa maso yammacin Najeriya inda shugaban ya fito ya jima ya na fama da hare-haren masu satar shanu da ma satar mutane tare da yin garkuwa da su domin neman kudin fansa.