Kotun Turkiyya ta ci gaba da tsare sojojin Girka biyu
July 17, 2018Talla
Wata kotun Turkiyya ta yanke hukuncin ci gaba da tsare sojojin Girka biyu bisa tuhuma kan leken asiri tun watan Maris. A wannan Talata kotun ta yi watsi da bukatar da lauyan sojojin ya gabatar matata kan neman bayar da belin sojojin biyu.
Kan wannan batu Firaminista Alexis Tsipras na Girka ya gana da Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya a gefen taron kungiyar tsaro ta NATO-OTAN a birnin Brussels na Beljiyam a makon jiya.