091211 Klimakonferenz Abschluss
December 9, 2011Bayan makonni biyu na tattaunawa, da sanyin safiyar ranar Lahadi mahalarta taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi a birnin Durban na ƙasar Afirka Ta Kudu, sun amince da wata yarjejeniya wadda a karon farko za ta tilastawa manyan ƙasashe ɗaukar matakin rage fitar da hayaƙi mai ɗumama yanayi. To sai dai masu fafatukar kare muhalli sun ce wannan matakin ba zai kai ga rage ɗumamar doron ƙasa ba.
Yarjejeniyar ta birnin Durban wadda ta tsawaita yarjejeniyar birnin Kyoto, ta farko da tilasta rage yawan iskar carbon, har zuwa shekara ta 2017, ta amince da kafa wani asusun taimakawa ƙasashe matalauta tinkarar matsalar sauyin yanayi, sannan ta tanadi wani shiri na cimma yarjejeniyar da za ta tilasta rage fid da hayaƙi mai guba.
Sai dai ƙananan tsibirai da ƙasashe masu tasowa dake fuskantar barazanar ambaliyar ruwan teku da mummunan yanayi sun yi ƙorafin cewa yarjejeniyar ta rasa wani nagartaccen tanadi da suke buƙata na tabbatar da makomarsu. Jan Kowalzig masanin muhalli ne na ƙungiyar agaji ta Oxfam reshen Jamus, ya ce taron na Durban ya gaza cimma ƙwaƙƙwarar matsaya akan batun tallafawa matakan tinkarar sauyin yanayi ga ƙasashe matalauta.
"Ba mu ji daɗi ba yadda aka kasa gabatar da wani nagartaccen tsarin ba da taimakon kuɗi. Duk da cewa yana akan jadawalin taron, amma ba a mayar da hankali kansa sosai ba. Shi yasa ba mu san inda aka dosa ba."
Duk da ƙarin lokaci na kwanaki biyu a taron, yarjejeniyar ba ta da inganci. A lokacin tattaunawar tarayyar Turai ta dage kan cimma wani kyakkyawan sakamako, inda har zuwa ƙarshen taron kwamishinar muhalli ta EU Connie Hedegaard ta kare wannan matsayi na ƙulla wata yarjejeniya da aiki da ita zai zama dole.
Ta ce: "Idan kana da babbar matsala, wata matsala ta duniya, wata matsala ta ƙasa da ƙasa, to wasu matakan ganin dama ba za su wadatar wajen magance wannan matsala ba."
Wakilai a taron da ya zama wani dandalin tattaunawa mafi tsawo akan sauyin yanayi na MDD cikin shekaru 20, sun amince daga baɗi za su fara aiki kan wata yarjejeniyar rage iskar dake ɗumama yanayi kafin shekarar 2015, wadda aiki da ita zai zama tilas kafin shekarar 2020.
Tarayyar Turai, Indiya, China da kuma Amirka suka amince da kalmomin yarjejeniya a sa'o'in ƙarshe na taron, dukkansu sun yi ikirarin samun nasara. A nasu ɓangaren masu fafatukar kare muhalli sun zargi gwamnatoci da ɓata lokaci wajen tsara kalmomin da za su a yi amfani da su wajen rubuta yarjejeniyar, inji Martin Kaiser na ƙungiyar Green Peace:
"Wata nasara ce ganin China da Indiya da Brazil da kuma Afirka Ta Kudu sun nuna shiga cikin yarjejeniyar kare muhalli. Amma har yanzu akwai hatsarin cewa a ƙarshe Amirka ba za ta shiga a dama da ita ba."
Duk da kurakuran dake cikin yarjejeniyar ta Durban, amma wani ci-gaba ne ga tattaunawar sauyin yanayin da ta cije shekaru da dama.
Mawallafi: Mohammad Nasir Awal
Edita : Abdullahi Tanko Bala