An kasa cimma matsaya a taron ministocin kudin EU
April 8, 2020Talla
A saboda takaddama da ake kan iya yawan tallafin da za a bayar don rage radadin Coronavirus, ministocin kudi na kasashen kungiyar tarayyar Turai EU sun dage zaman tattaunawarsu bayan sun shafe sa'o'i 16 ba tare da sun cimma matsaya ba.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban kungiyar Eurogroup, Mario Centeno ya ce a ranar Alhamis za su ci gaba da tattaunawar. Ya kara da cewa an kusa cimma matsaya, amma har yanzu ba a kai gaci ba.
Manufa ita ce samar da kwakkwaran shirin yaki da annobar Covid-19. Shirin dai ana sa ra zai ci kudi Euro miliyan dubu 500. Babban cikas kamar yadda mahalarta taron suka nunar shi ne takaddama game da daukar nauyin biyan bashi da kungiyar gaba daya za ta yi.